Isa ga babban shafi
Coronavirus

Coronavirus ta hana 'yan siyasar Najeriya zuwa asibitin Turai

Shekaru sama da 30 kenan da Najeriya ta koma mulkin dimokiradiya, amma har yanzu manyan jami’an gwamnatin kasar sun gaza inganta bangaren kiwon lafiya a matakai daban daban ta hanyar samar da kayan aiki na zamani da kuma kwararrun jami’an da za su rika kula da lafiyar jama’a.

Likitocin Najeriya na ficewa daga kasar saboda rashin ingantattun kayayyakin kiwon lafiya
Likitocin Najeriya na ficewa daga kasar saboda rashin ingantattun kayayyakin kiwon lafiya Getty image/ David Sacks
Talla

'Yan siyasar sun dauki  kasashen Turai da na Larabawa da Amurka a matsayin wuraren zuwa duba lafiyarsu, yayin da suka bar talakawansu suna mutuwa wajen neman lafiyarsu a asibitocin da ba su da inganci.

Wannan matsalar ta shafi shugabannin kasar da ministoci da kuma gwamnonin jihohi da kuma tarin jami’an gwamnati da suka zama attajirai.

Tun bayan da aka samu mutun na farko da ya kamu da cutar coronavirus a Najeriya, wadannan shugabannin suka daina tafiye-tafiye, inda suka koma amfani da wadannan asibitocin da ba su da inganci saboda a yanzu ba su da zabi.

Wannan ya biyo bayan matakan da kasashe da dama suka dauka na rufe iyakokinsu da dakatar da sufurin jiragen sama, yayin da ita ma Najeriya ta dauki irin wannan matakin.

Masana kiwon lafiya sun ce, Najeriya ba ta da isassun kayan aiki a asibitocin gwamnati, kuma sauran asibitoci masu zaman kansu basu sun yi wa takawa tsada.

Alkaluma sun nuna cewa, Najeriya na dauke da likitoci 75,000, masu taimaka musu 180,709 da masana harkar magunguna 25,000 kamar yadda ma’aikatar lafiyar kasar ta sanar, adadin da aka bayyana cewar ya gaza wajen kula da lafiyar al’ummar kasar kusan miliyan 200.

Yanzu haka ana ta cacar-baka kan rashin isassun wuraren gwajin cutar coronavirus a Najeriya saboda karancinsu, inda alkaluma suka nuna cewar baya ga Abuja, babu wurin gwajin a yankin arewacin kasar, yayin da sauran suke yankin kudu amma kuma basu taka-kara-sun-karya ba.

Ganin irin halin da wadannan shugabannin siyasa suka samu kansu a ciki musamman yadda suka saba tafiya kasashen waje domin a duba su kan cutar da ba ta wuce ciwon kai da makamantarsu ba. Watakila a yanzu za su mayar da hankali wajen inganta asibitocin jihohi da na tarayya domin kula da lafiyar jama’a da suma kansu.

Abin sani anan shi ne, yanzu dai manyan jami’an gwamnatin daga shugaban kasa zuwa ministocinsa da ba sa iya kwanaki 5 a jihohinsu, da ma gwamnonin jihohi, sun kwashe sama da kwanaki 10 basu bar yankunansu ba saboda wannan annoba.

Ko su shugabannin kasashen duniya da suka saba zirga zirga zuwa kasashen duniya coronavirus ta yi musu dabaibayi wadda ta sa su zama a gida saboda tsoron wannan cuta.

Masana na kallon daukar wannan matakin gyarar asibitocin ka iya bai wa likitocin Najeriya kwarin gwuiwar ci gaba da zama a kasashensu domin yin aiki, sabanin yadda suke tsallakawa suna tafiya Turai da Amurka da kasashen Larabawa domin yin aiki inda ake kula da su tare da samun albashi mai inganci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.