Isa ga babban shafi
Najeriya

Babu coronavirus a jiharmu-Gwamnatin Jigawa

Gwamnatin jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya ta musanta labarin bullar cutar COVID-19 a jihar da wasu kafofin yada labarai suka wallafa.

Gwamnan Jigawa Alhaji Badaru Abubakar
Gwamnan Jigawa Alhaji Badaru Abubakar jigawastate.gov.ng
Talla

Kwamishin Lafiyar Jihar kuma shugaban Kwamitin Yaki da Cutar Corona Dr. Abba Zakari ya bayyana haka a yayin zantawarsa da RFI Hausa.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren bayanin da ya yi Abubakar Isa Dandago.

A cewar mahukuntan jihar, mutumin da ake magana a kansa duk da cewa dan asalin jihar Jigawar ne, amma a can Kano aka dauki jininsa kuma aka tabbatar ya kamu da cutar jim kadan da dawowarsa daga Lagos, kuma bisa doka ana lissafa masu cutar ne a wurin da aka yi musu gwaji.

Sai dai gwamnatin Kano ta mika mutumin ga hukumomin lafiyar Jigawa don ci gaba da kulawa da shi, amma duk da haka gwamnatin Jigawa na ci gaba da lissafa shi cikin masu dauke da coronavirus a Kano.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.