Isa ga babban shafi
Najeriya

Mun kashe 'yan Boko Haram sama da 100-Sojin Najeriya

Rundunar Sojin Najeriya ta yi shelar kashe mayakan Boko Haram 105 a samamen da dakarunta suka kaddamar kan maboyar 'yan ta'addar da ke Bunu-Gari a Jihar Yobe.

Wasu daga cikin sojojin Najeriya da ke yaki da Boko Haram
Wasu daga cikin sojojin Najeriya da ke yaki da Boko Haram REUTERS/Warren Strobel
Talla

Daraktan Yada Labaran Rundunar, Kanar Sagir Musa ya sanar da haka a daidai lokacin da shugaban sojin Janar Yusuf Tukur Buratai ya tare a arewa maso gabashin kasar  domin ganin an murkushe mayakan kungiyar baki daya.

Kanar Musa ya ce, runduna ta biyu ta dakarun da ke yaki da kungiyar Boko Haram a karkashin Birgediya Janar Lawrence Araba, ta samu nasarar kashe mayakan sakamakon bayanan sirri da aka tsegunta musu.

Daraktan Yada Labaran ya ce, shugaban rundunar sojin Janar Buratai ya bayyana farin cikinsa da wannan gagarumar nasara lokacin da ya ziyarci dakarun domin ganewa idansa da kuma jinjina musu kan wannan nasara.

Janar Araba ya kuma nuna wa Janar Buratai tarin makaman da suka kwace da suka hada da bindigogi masu sarrafa kansu da kuma motar yaki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.