Isa ga babban shafi
Najeriya-Kaduna

Gwamnonin Arewa sun yanke shawarar kawo karshen Almajiranci - El-Rufa'i

Gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufa’I ya sanar da kawo karshen tsarin karatun Almajirci a daukacin jihar, matakin da yace shi ne daukacin gwamnonin arewacin Najeriya suka cimma matsayar dauka.

Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa'i.
Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa'i. TheCable
Talla

Yayin wata zantawa da kafar talabijin ta Channels TV El Rufa’i ya kuma ce tuni nazari yayi nisa kan samar da waso dokoki da kuma sauya fasalin wasunsu, domin tabbatar da cewa, tsarin karatun na almajirci bai sake farfadowa ba a jihar.

Gwamnan Kadunan, yace a halin da ake ciki gwamnatinsa tayi nasarar mayarda almajirai sama da dubu 30 zuwa jihohin da suka fito.

A baya bayan gwamnonin jihohi a Najeriya musamman a arewacin kasar sun yi ta musayar maida almajirai zuwa ainahin garuruwansu, kuma bulllar annobar COVID-19 ta karfafa shirin da wasunsu suka ce dama suna shirin aiwatarwa na kawo karshen tsarin karatun almajiranci, matakin da zai magance matsalar barace-barace da kananan yara ke yi akan tituna da layukan unguwanni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.