Hana kwararru gwajin cutar corona a Kogi da Cross River kuskure ne babba - Likitoci
Kungiyar likitocin Najeriya ta nuna takaicinta kan yadda gwamnatocin Cross River da Kogi suka hana cibiyar dake yaki da yaduwar cutuka ta Najeriyar NCDC gudanar da gwaje-gwajen annobar coronavirus a jihohinsu.
Wallafawa ranar:
Wannan na zuwa ne bayanda gwamnonin suka yi zargin za a yi amfani da matakin gudanar da gwaje-gwajen wajen shigar musu da cutar.
Yayin zantawa da sashin Hausa na RFI, Dakta Yusuf Abdu Misau, malami a Jami’ar Fasaha ta jami'ar Abubakar Tafawa Balewa dake Bauchi, kuma daya daga cikin kungiyar likitocin Najeriyar, yace bayyana matakin da gwamnonin jihohin na Cross River ta Kogi suka dauka a matsayin kuskure babba.
Dakta Misau yace irin haka taso faruwa a Jihar Kano, inda da da fari mafi rinjayen al’ummar garin ke ganin cutar coronavirus bata shiga jihar ba, amma bayan soma aikin tawagar kwararrun likitoci sai labara ya sha banban, zalika ya zargi gwamnonin Kogi da Cross River da sanya siyasa cikin lamarin.
Dakta Yusuf Abdu Misau kan matakin jihohin Kogi da Cross River na hana kwararru yiwa mutane gwajin cutar corona
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu