Isa ga babban shafi
Najeriya

Mutane 23 sun rasa rayukansu dalilin hadarin tankar mai a Kogi

Hukumomin Najeriya sun tabbatar da mutuwar mutane 23 a hadarin tankin man da aka samu a Lokoja dake Jihar Kogi, yayin da mazauna yankin ke cewa adadin na iya ninkawa.

yadda hadarin tankar mai yayi sanadin konewar ababen hawa a garin Lokojadake jihar Kogi a Najeriya
yadda hadarin tankar mai yayi sanadin konewar ababen hawa a garin Lokojadake jihar Kogi a Najeriya Daily Trust
Talla

Rahotanni sun ce daga cikin wadanda suka rasa ‘yan uwansu harda wani da ake kira Idris Yusuf, wanda yaransa guda 6 suka kone a cikin mota lokacin da suke tafiya makaranta, yayin da wani da ake kira Samson ya rasa matarsa da yaransa guda 3 a hadarin.

Ganau sun ce hadarin ya auku ne, bayan da ga alama matukin tankar man ya rasa birki, abinda ya sanya shi yin taho mu gama da wasu jerin motoci, inda akalla biyar daga ciki suka kone.

Wasu dai na fargabar adadin wadanda suka rasa rayukansu ka iya zarta 50, la'akari da cewar akwai tarin jama'ar da ke gefen hanya suna jiran shiga motocin haya domin isa wuraren ayyuka ko lamurransu na yau da kullum.

Domin jin halin da ake ciki, sashin Hausa na RFI ya tattauna da Ishaq Dan Imam, dan jarida dake zaune a garin na Lokoja.

00:51

Ishaq Dan Imam, dan jarida kan hadarin tankar mai da ya halaka mutane da dama a Lokoja

Nura Ado Suleiman

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana kaduwar sa da hadarin, inda ya mika sakon ta’aziyya ga ‘yan uwan wadanda hadarin ya ritsa da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.