Isa ga babban shafi

Najeriya ta rasa jagoranci na gari -NWGPG

Wasu fitattun jagororin al’umma a Najeriya karkashin kungiyar masu rajin tabbatar da zaman lafiya da samuwar ingatacciyar gwamnati ta (NWGPG) sun koka kan cewar yanzu haka kasar na cikin mawuyacin hali, da ke nuna tamkar babu gwamnatin da ke jagorantar ta.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. REUTERS/Carlo Allegri
Talla

Daga cikin fitattun mutanen da suka yi wannan gargadi akwai, Farfesa Jibril Ibrahim, Dakta Usman Bugaje, janar Martin Luther Agwai mai ritaya, tsohon shugaban hukumar zaben Najeriya Farfesa Attahiru Jega, John Cardinal Onaiyekan, da kuma Ambassador Zango Abdu.

Cikin sanarwar da suka fitar a jiya Alhamis, jagororin sun kare matsayinsu na cewar gwamnatin Najeriya ta gaza ne da hujjojin yadda matsalar cin hanci da rashawa ke kara yin muni, wanda kuma a daidai lokacin gwamnati ke kokarin rushe hukumomin da ke yakar matsalar, abinda ya baiwa masu almundahana damar cin karensu ba babbaka.

Fitattun mutanen sun kuma koka kan yadda ake cigaba da samun baraka tsakanin ‘yan Najeriya ta fuskokin addini, da kabilanci, sai kuma rashin kaykkyawar alaka musamman ta musayar bayanai tsakanin gwamnati da ‘yan kasa, sakamakon yin watsi da ta yi da kiraye-kirayen sake fasalta tsarin shugabanci.

Sai kuma matsalolin tsaro na hare-haren ‘yan bindiga da satar mutane dake karuwa a sassan Najeriya, da kuma matasalar book haram da taki ci taki cinyewa, dan haka lokaci yayi da ‘yan Najeriya za su hada kai wajen tunkarar kalubalen da ke gabansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.