Isa ga babban shafi
Najeriya-Boko Haram

Kotun Daular Larabawa ta daure 'yan Najeriya saboda daukar nauyin Boko Haram

Kotun daukaka kara a Daular Larabawa ta daure wasu 'yan Najeriya guda 6 da aka samu da laifin bai wa kungiyar Boko Haram kudaden gudanar da harkokin ta.

Jagoran mayakan Boko Haram Abubakar Shekau tare da mayakansa
Jagoran mayakan Boko Haram Abubakar Shekau tare da mayakansa © AFP PHOTO / BOKO HARAM
Talla

Jaridar Daily Trust da ake wallafawa a kasar ta bayyana sunayen biyu daga cikin su da aka yanke wa hukuncin daurin rai da rai da suka hada da Surajo Abubakar Mahmud da Saleh Yusuf Adamu, yayin da sauran 4 kuma da aka daure shekaru 10-10 a gidan yari suka hada da Ibrahim Ali Alhassan da Abdurrahman Ado Musa da Bashir Ali Yusuf da kuma Muhammad Ibrahim Isa.

Jaridar ta ce an yi wa wadannan mutane shari’ar ce a shekarar 2019 inda aka same su da laifi aka kuma yanke musu hukunci a kai.

Takardun kotun sun bayyana cewar tsakanin shekarar 2015 zuwa 2016, wadanda aka yanke wa hukuncin sun yi ta aikewa da kudade ga kungiyar da yawan su ya kai Dala dubu 782,000.

Batun gano masu daukar nauyin kungiyar boko haram ya gagari hukumomin Najeriya inda bayan shekaru 11 aka gaza hukunta mutanen da ake zargi da bai wa kungiyar kudaden gudanar da harkokin ta.

Sai dai kuma Jaridar Daily Trust ta jiyo ta bakin 'yan uwan mutanen da aka dauren na cewa yarfe aka musu domin bata musu suna, domin kuwa suna gudanar da sana’ar canja kudi ne lokacin da aka kama su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.