Isa ga babban shafi
Amurka-Najeriya

Amurka ta sanya Najeriya cikin kasashen dake dakile ‘yancin addini

Kasar Amurka ta sanya sunan Najeriya cikin jerin kasashen dake kin baiwa jama’a ‘yancin gudanar da addininsu, sakamakon korafin da Kiristoci ke yi saboda matsalolin tsaro.

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump MANDEL NGAN / AFP
Talla

Sakataren harkokin wajen kasar Mike Pompeo, ya bayyana Najeriya a matsayin kasar da suke bayyana damuwar su dangane da ‘yancin gudanar da addini.

Pompeo yace wannan mataki da suka dauka kan Najeriya na nuna cewar duk lokacin da aka hana mutane ‘yancin gudanar da addininsu, za su dauki mataki akai.

Sakataren harkokin wajen Amurkan ya ce suna daukar irin wannan matakin ne domin kunyata kasashen duniya da suka gaza magance matsalar ta hana mutane ‘yancin gudanar da addininsu.

Sauran kasashen da Amurka ta sanya cikin jerin wadanda ke take hakkin ‘yancin gudanar da addini sun hada da China, Iran, Saudi Arabia, Myanmar, Eritrea da Korea ta Arewa da Pakistan.

Sai dai rashin sanya India cikin jerin wadannan kasashen ya fusata wasu inda suke ganin Amurkan ba ta yi adalci ba, la’akari da halin da Musulmi ke ciki a karkashin gwamnatin Fira Minista Narendra Modi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.