Isa ga babban shafi
Muhallinka Rayuwarka

Makomar noma a Zabarmari bayan kisan gillar da mayakan Boko Haram suka yiwa manoma

Wallafawa ranar:

A makon da ya gabata shirin Muhallinka Rayuwarka ya leka yankin Zabarmari dake jihar Borno inda mayakan Boko Haram suka yiwa manoma sama da 70 kisan gilla ta hanyar yankan rago, lamarin da ya tayar da hankali a ciki da wajen Najeriya, ganin cewa farmakin ya zo ne a daidai gwamnatin jihar ke kokarin daidaita lamurra ta hanyar mayar da mutane muhallansu da suka tserewa a dalilin tashin hankalin na Boko Haram.

Yadda aka yi jana'izar manoman da mayakan Boko Haram suka yiwa kisan gilla a yankin Zabarmari.
Yadda aka yi jana'izar manoman da mayakan Boko Haram suka yiwa kisan gilla a yankin Zabarmari. REUTERS/Ahmed Kingimi
Talla

A makon jiya mun tattauna da wakilinmu a jihar ta Bornon Bilyaminu Yusuf kan halin da ake ciki musamman manoman da farmakin na baya bayan nan ya shafa, a yau kuma zamu dora da rahoton da wakilanmu ya aiko mana kan al’amarin

Shirin ya kuma waiwayi barazanar da tsintsaye da sauran kwari ke yiwa amfanin gona a wuraren da aka samu sukunin yin noma a sassan Najeriya, inda rahotanni daga wasu yankunan jihar Sokoto suka bayyana yadda a wasu lokutan kwari da tsintsayen ke barna a gonaki, lamarin da shima ke zaman wata babbar barazana ga shirin samar da abinci a Najeriyar, matsawar ba a tashi tsaye ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.