Isa ga babban shafi
Najeriya

Adadin sabbin masu kamuwa da Covid-19 ya fara tsananta a Najeriya

Najeriya ta kama hanyar sake fuskantar annobar korona ganin yadda masu kamuwa da cutar ke karuwa, inda a jiya kawai aka samu mutane 930 da suka harbu da ita.

Wani da ake yiwa gwajin Coronavirus a Najeriya.
Wani da ake yiwa gwajin Coronavirus a Najeriya. Reuters/Afolabi Sotunde
Talla

Alkaluman da Hukumar yaki da cututtuka a Najeriya ta gabatar sun nuna cewar a cikin sa’oi 24 da suka gabata, an samu mutane 930 da suka harbu da cutar, wanda ya zarce 796 da aka gani kwanaki 5 da suka gabata.

Kafin dai sake dawowar cutar Najeriya bata taba ganin mutanen da suka wuce 745 tun daga ranar 19 ga watan Yuni, abinda ke nuna cewar cutar sannu a hankali na sake dawowa.

Alkaluman sun bayyana cewar Jihar Lagos ke sahun gaba wajen samun sabbin wadanda suka kamu da cutar, inda take da 279, sai Abuja mai 179, sannan Plateau mai 62.

Sauran sun hada da Kaduna mai 62, Kano da Katsina nada 52-52, Imo da Jigawa 42-42, Rivers 38, Kwara 30, Nasarawa 19, Yobe 15, Ogun 13, Borno 10.

Ya zuwa yanzu cutar ta kama mutane 75,062 a fadin Najeriya, kuma 1,200 daga cikin su sun mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.