Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan bindiga sun halaka jami'an tsaro 2 a Jigawa

‘Yan bindiga sun halaka jami’an ‘yan sanda 2 tare da jikkata guda a karamar hukumar Garki dake Jigawa.

Hoton mai kwatanta 'yan bindiga.
Hoton mai kwatanta 'yan bindiga. Information Nigeria
Talla

Yayin tabbatar da aukuwar lamarin kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Abdu Jinjiri yace tawagar jami’ansu ta kaiwa maboyar ‘yan bindigar samame ne a karamar hukumar Gumel don kawo karshen addabar al’ummmar yankin da suke yi, inda batagarin suka yi musu kwanton Bauna.

Bayan musayar wuta ne jami’an ‘yan sanda suka rasa mutane biyu, yayin da suka kashe guda daga cikin ‘yan bindigar.

A wani labarin kuma kakakin ‘yan sandan na Jigawa, ya tabbatar da rahoton sace wata matar aure mai shayarwa da ‘yan bindiga suka yi garin Gujungu dake karamar hukumar Taura, da misalin karfe 2 na daren wayewar ranar Asabar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.