Isa ga babban shafi
Najeriya-Kaduna

Sojin Najeriya sun halaka 'yan bindiga da dama a Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna dake tarayyar Najeriya tace sojoji sun samu nasarar halaka ‘yan bindiga da dama, a karamar hukumar Birnin Gwari.

Wani jirgin yakin Najeriya.
Wani jirgin yakin Najeriya. @DefenseNigeria
Talla

Yayin wata ganawa da manema labarai, kwamishin tsaron cikin gidan jihar ta Kaduna Samuel Aruwan, yace sojin saman Najeriya sun halaka ‘yan bindigar ne a kauyukan Farin Ruwa, Saulawa da kuma Kuduru, a yayin da suke zirga-zirga kan babura.

Aruwan yace dakarun Najeriyar sun halaka wasu karin ‘yan bindigar ne kuma a Unguwan yako, yayin da suke kora shanu zuwa Kuduru.

Baya ga farmaki kan ‘yan bindigar, sojin saman Najeriyar sun kuma rika yin sintiri a wasu yankunan da suka yi kaurin suna wajen fuskantar matsalar hare-haren barayin shanun, da suka hada da hanyar Kaduna zuwa Abuja, Rijana, Kateri, Jere, Buruku da kuma wasu sassan cikin garin Kaduna, sintirin da gwamnatin jihar ta Kaduna tace zai cigaba da gudana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.