Isa ga babban shafi
Najeriya

Kashi 69 na 'yan Najeriya sun yadda cutar Korona gaskiya ce - Rahoto

Wani bincike da wata kungiya tayi a Najeriya ya nuna cewar kashi daya bisa 5 na al’ummar kasar basu amince da wanzuwar cutar korona ba, duk da dibar rayukan da take a kasashen duniya.

Wasu 'yan Najeriya sanye da takunkuman rufe baki da hanci a unguwar Ojodu-Berger dake birnin Lagos, don dakile yaduwar annobar Coronavirus. 4/5/2020.
Wasu 'yan Najeriya sanye da takunkuman rufe baki da hanci a unguwar Ojodu-Berger dake birnin Lagos, don dakile yaduwar annobar Coronavirus. 4/5/2020. AFP
Talla

Binciken da kungiyar SBM Intel ta gudanar a Jihohin Najeriya 36 da birnin Abuja, ya nuna cewar kashi kusan 69 na Yan Najeriya sun amince da cutar, kuma akasarın su na daukar matakan kariya, yayin da kashi kusan 14 da rabi ke shakkun wanzuwar cutar, sai kuma kashi kusan 17 dake da matsayin cewar babu cutar gaba daya, sai dai yaudara kawai da ake musu.

Daga cikin Jihohin da mutane suka fi amincewa da wanzuwar cutar akwai Ekiti da Enugu da Kogi da Nasarawa da kuma Sokoto, sai kuma Jihohin Abia da Gombe da mutane suka goyi bayan sake killace jama’a idan aka samu karuwar masu harbuwa da cutar.

Binciken ya gano wasu mutane dake hasashen cewar maganin rigakafin da aka samar, wani yunkuri ne kawai na rage yawan jama’a a Najeriya, yayin da wasu kuma ke nuna shakku kan sahihancinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.