Isa ga babban shafi
Najeriya-Oyo

Zaman tankiya na karuwa tsakanin makiyaya da 'yan gari a Oyo

Rahotanni daga jihar Oyo dake kudancin Najeriya sun ce mutane biyu ake fargabar sun rasa rayukansu, bayan da rikici ya barke yankin Igangan dake karamar hukumar Ibarapa ta Arewa.

Wasu Fulani makiyaya a Najeriya
Wasu Fulani makiyaya a Najeriya REUTERS/Akintunde Akinleye
Talla

Bayanai sun ce fadan ya auku ne a ranar Juma’a, bayan da wani jagoran matasa dake fafutukar kare hakkin Yarbawa Sunday Igboho tare da magoya bayansa suka yi yunkurin tilasta korar Fulani makiyaya dake zaune a garin na Igangan ciki har da sarkinsu, wadanda suka zarga da hannu cikin matsalolin tsaron da suka addabi sassan jihar Oyo.

Kawo yanzu babu karin bayani kan rikicin a hukumance, sai dai bangaren makiyayan yayi ikirarin an kashe musu mace daya, yayin da magoya bayan Sunday Igboho suka rasa mutum guda.

Tun a ranar Alhamis aka soma samun tankiya garin na Igangan dake jihar Oyo, bayan da jagoran matasan dake fafutukan kare hakkin Yarbawa ya baiwa Fulani makiyaya wa’adin kwanaki kalilan dasu fice daga jihar saboda zarginsu da aikata muggan laifuka.

Sai dai a jiya Juma’a Gwamnan jihar Seyi Makinde yayi gargadin ba zai lamunci kyale wani ko wata kungiya ta haddasa tashin hankali ta hanyar take hakki, ko korar wata kabila ba.

A ranar Litinin da ta gabata gwamnan Jihar Ondo Rotimi Akeredolu ya baiwa makiyaya wa’adin kwanaki 7 da su fice daga dazukan jiharsa saboda zarginsu da hannu a matsalolin tsaron da suka hada da satar mutane da kuma hare-haren ‘yan bindiga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.