Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya za ta haramta saukar jirage daga Daular Larabawa da Netherlands

Gwamnatin Najeriya na tunanin haramtawa jiragen saman kasashen Daular Larabawa da Netherlands sauka a kasar saboda matakan da kasashen suka dauka kan bakin da ke zuwa kasashen su sakamakon cutar corona.

Filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja a Najeriya.
Filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja a Najeriya. The Guardian Nigeria
Talla

Shugaban hukumar kula da sufurin jiragen sama Musa Nuhu ya ce wadannan kasashe guda biyu sun bukaci duk wani fasinja daga Najeriya ya gabatar da takardar gwajin cutar korona da aka masa sa’oi kafin barin Najeriya sabanin sa’oi 72 da kasashen duniya suka amince da shi.

Najeriya ta ce muddin wadannan kasashe suka hakikance sai an bi yadda suke so, toh babu abinda Najeriya za ta yi da ya wuce ta hana jiragen saman kasashen zuwa cikin kasar ta.

Jami’in ya ce babu yadda za a yi jiragen da ke zuwa Najeriya su gabatarwa kasar ka’idojin da suke so abi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.