Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan bindiga sun kashe mutane dubu 30 a Najeriya

Wani binciken masana a Najeriya ya nuna cewar akalla mutane dubu 30 suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren 'yan bindiga a cikin shekaru 10 da suka gabata, yayin da sama da miliyan 3 suka tsere daga gidajensu.

Alamun 'yan bindiga masu garkuwa da mutane a Najeriya
Alamun 'yan bindiga masu garkuwa da mutane a Najeriya Daily Trust
Talla

Farfesa Magaji Garba, shugaban Jami’ar Gusau ya bayyana haka cikin kasidar da ya gabatar mai taken ‘Ayyukan 'Yan Bindiga da Tsaron Kasa a Najeriya’ a wajen wani taron kasa da ya gudana a birnin Gusau da ke jihar Zamfara.

Shugaban Jami’ar ya ce ya zama wajibi duk masu ruwa da tsaki a Najeriya su hada kai wajen lalubo hanyar wannan matsala wadda ta zama ruwan dare a yankunan karkara wanda kuma ke barazana ga harkokin yau da kullum ga jama’ar Najeriya.

Farfesa Garba ya bayyana cewar Hukumar Jami’ar Gusau za ta hada kai da duk hukumomi da masu ruwa da tsakin da suke bukata wajen kawo karshen wannan matsalar.

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle da ke jawabi wajen taron, ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da aiwatar da tsarin ta na tattaunawa da ‘yan bindigar da kuma kai hari kan wadanda suka ki bada kai domin raba jihar da masu aikata laifuffuka.

Matawalle ya ce wannan hanyar da ya dauka ta taimaka sosai wajen bude kofa ga masu bukatar ajiye makamai domin tattaunawa da su da zummar samun maslaha, inda yake cewa ta wannan hanyar ce kawai za a shawo kan matsalar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.