Isa ga babban shafi

El Rufa'i ya nemi Gwamnonin kudancin Najeriya su soki hare-hare kan Fulani

Gwamnan Jihar Kaduna da ke Najeriya Malam Nasir El Rufai ya bukaci takwarorin sa da ke yankin kudancin kasar su fito fili wajen sukar mutanen da ke kai hari kan Fulani makiyaya, inda ya ke cewa kowanne dan kasa na da hurumin zaman lafiya a duk inda yake so.

Gwamnan jihar Kaduna a Najeriya Malam Nasir El-Rufa'i.
Gwamnan jihar Kaduna a Najeriya Malam Nasir El-Rufa'i. kdsg.gov.ng
Talla

El Rufai ya ce bai dace a bar ayyukan 'yan bindiga da bata-gari ya yaba kan Najeriya ba, inda ya bayyana cewar aikin Gwamnonin ne su kare lafiya da dukiyoyin daukacin 'yan Najeriya da ke zama a Jihohin su.

Gwamnan ya ce a irin wannan yanayi mai wahala ya dace a kare lafiyar kowanne dan kasa wajen samar masa da tsaro da kuma kare dukiyarsa, yayin da ya ce yiwa wata kabila lamba ana kyamar ta saboda laifin da wasu 'yan kalilan ke aikatawa zai taimaka ne kawai wajen haifar da tashin hankali da kuma rashin zaman lafiya.

El Rufai ya bayyana damuwa kan yadda ake yada wani faifan bidiyo yanzu ta kafar sada zumunta wanda ke nuna yadda ake kai hari kan Fulani da dukiyoyin su a kudancin Najeriya wanda ya ce na iya tunzura jama’a.

Gwamnan ya ce 'yan Jihar Kaduna da dama sun tintibe shi domin sanin gaskiyar abinda bidiyon ya kun sa, saboda zargin cewar masu kai hare haren na samun goyan bayan shugabannin yankunan su.

El Rufai ya ce duk da ya ke bai iya tabbatar da sahihancin bidiyon ba, amma abinda ke ciki na dauke da tashin hankali kuma yana iya shafar zaman lafiyar Najeriya.

Sai Gwamnan ya yi kira ga zababbun shugabannu da wadanda aka nada a sasasn Najeriya da suyi aiki da kundin tsarin mulki wajen kare lafiya da dukiyoyin 'yan kasa, inda ya ke cewa su a Kaduna sun koyi hankali dangane da irin rikice rikicen da Jihar ta gani da kuma illar da ya yi mata wajen rikicin da ake dangantawa tsakanin baki da yan kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.