Isa ga babban shafi
Najeriya-Kano

Gwamnatin Kano ta haramtawa Shiekh Abduljabbar yin wa'azi

Gwamnatin Kano ta dakatar da Shiekh AbdulJabbar Nasiru Kabara daga gabatar da duk wani nau’in wa’azi a fadin jihar, tare da umarnin rufe masallacinsa mai suna As-habul kahfi dake unguwar Sani Mai Nagge.

Shiekh Abdujabbar Nasiru Kabara
Shiekh Abdujabbar Nasiru Kabara YouTube
Talla

Kwamishinan watsa labaran jihar ta Kano Muhammad Garba ne ya sanar da hakan a daren ranar Laraba, inda yace matakin ya soma aiki ne anan take.

yayin ganawa da manema labarai cikinsu har da wakilinmu Abubakar Isa Dandago, kwamishinan yace matakin kan Shiekh Abduljabbar ya zama dole, sakamakon rahotannin kalaman tunzura jama’a da rashin kan gado da fitaccen malamin ke yi, yayin gabatar da wa’azinsa.

00:57

Kwamishinan watsa labaran jihar Kano Muhammad Garba kan dakatar da wa'azin Shiekh Abduljabbar Nasiru Kabara

Abubakar Issa Dandago

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.