Abdul-Jabbar makaryaci ne-Ganduje
Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana Malamin addinin Islaman nan, Sheikh Abdul-Jabbar Nasiru Kabara a matsayin makaryaci kuma mayaudari, yana mai musanta ikirarin malamin na cewa Kwamishinan Ilimin jihar ya tabbatar da zaluntar sa.
Wallafawa ranar:
Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakken bayanin Ganduje
Martanin Ganduje ga Abdul-Jabbar
Jim kadan da dakatar da shi daga gabatar da wa’azi da huduba, Abdul-Jabbar ya shaida wa manema labarai cewa, an yi hira da Kwaminishin Ilimin Jihar Kano wanda ya tabbatar da cewa, an zalunci malamin a cewarsa.
Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren bayanin Abdul-Jabbar.
Muryar Abdul-Jabbar
Wata majiya ta shaida wa manema labarai cewa, a halin yanzu gwamnatin Kano wadda ta gana da Majalisar Malaman Jihar, ta bukaci malaman da su duba ayoyin Al-Kur’ani da Hadisan Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam don fitar da hukuncin da ya dace kan Abdul-Jabbar.
Dakataccen malamin ya bayyana cewa, malaman jihar Kano sun shigar da siyasa a cikin addinin Musulunci.
Tuni Jami’an tsaro suka killace gidansa da masallacinsa na Ashabul-Kahfi, sannan kuma aka yi masa daurin talala.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu