Isa ga babban shafi
Najeriya

Tabbas shanu sun shiga gida na, 'yan sanda sunyi karya - Soyinka

Fitatcen Marubucin Najeriya Farfesa Wole Soyinka ya zargi rundunar 'Yan Sandan Najeriya da yin karya cewar shanu basu shiga gidan sa ba kamar yadda yayi ikrari.

Fitaccen Marubucin Najeriya Wole Soyinka
Fitaccen Marubucin Najeriya Wole Soyinka © DR
Talla

Sanarwar da Soyinka ya rabawa manema labarai ta bayyana matsayin 'Yan Sandan a matsayin karya, inda yake cewa tabbas shanu sun shiga gidan sa kafin a kore su.

Rundunar 'Yan sanda tace saniya guda ce ta shiga gidan marubucin, kuma Baturen 'Yan Sandan Yankin ya ziyarci gidan na sa domin ganewa idan sa abinda ya faru, kuma babu abinda aka lalata.

Sai dai Soyinka yaki amincewa da rahotan 'Yan Sanda, inda yake cewa garken shanu ne suka shiga gidan sa, kuma yana da hotan dake tabbattar da haka.

Shehun malamin yace da kan sa suka kama wasu daga cikin shanun suka mikawa 'Yan sanda, yayin da makiyayan suka gudu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.