Isa ga babban shafi
Najeriya-Buhari

Najeriya ta kafa kamfanin gudanar da manyan ayyukan raya kasa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da shirin kafa wani kamfani da zai gaggauta samar da kayayyakin more rayuwa wanda zai ci kudin da ya kai sama da Dala biliyan 2 da rabi.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. Nigeria Presidency/Handout via REUTERS
Talla

Kamfanin da aka yiwa suna Infra-Co zai zama daya daag cikin manyan kamfanonin da zai dinga samar da kudaden da za a dinga ayyukan raya kasa a Afirka wanda kuma zai mayar da hankali ne wajen aiki a Najeriya.

Mai Magana da yawun mataimakin shugaban kasar Yemi Osinbajo ya ce wannan kamfanin da zai dinga samar da kudaden da za a gina hanyoyi da samar da ruwan sha da hanyoyin jiragen kasa da wutar lantarki da makamantan su zai yi hadin gwuiwa da ‘yan kasuwa, kuma babban bankin Najeriya da hukumar zuba jari ta kasa da hukumar samar da kudade ta Afirka za su samar da kudaden da ake bukata.

A shekarar da ta gabata Majalisar Dattawan Najeriya ta amincewa gwamnati ciwo bashin Dala biliyan 23 daga kasashen waje domin gudanar da manyan ayyukan raya kasa, matakin da ake ganin zai taimaka wajen samar da ayyukan yi da kuma fitar da kasar daga koma bayan tattalin arziki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.