Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya: 'Yan sanda sun kama masu zanga - zanga da dama a kofar Lekki

‘Yan sandan Najeriya sun kama masu zanga- zanga da dama a birnin Lagos a yau Asabar, bayan da suka yi kokarin gudanar da zanga – zangar neman adalci ga wadanda dirar mikiya da jami’an tsaro suka yi wa masu gangami a shekarar da ta gabata ta ritsa da su.

Wani ofishin 'ya sanda a Najeriya.
Wani ofishin 'ya sanda a Najeriya. AFP
Talla

Masu fafutuka sun yi kira ga zanga zanga a ranar Asabar, bayan da ,wata kotu ta musamman ta yi umurnin a sake bude babbar kofar shiga birnin Lekki, inda nan ne suke zargin jami’an tsaro da bude wa masu zanga zanga wuta.

A shekarar da ta gabata, zanga zangar da aka wa lakabi da #EndSARS, wacce akasari matasa suka kaddamar don nuna rashin amincewa da cin zalin da ‘yan sanda ke yi, ya dakile al’amura a birnin na Lagos a watan Oktoba.

Zanga zangar ta samu goyon bayan manyan mawaka da jaruman fina finai da dai sauran fitattun mutane, musammamn daga kudancin Najeriya.

A yau Asabar, ‘yan sanda sun kama mutane dama, suka kuma jefa su a bakar motar da ake daukar masu aikata laifuka a yankin Lekki Tollgate, inda tun a ranar Juma’a jami’an tsaro ke sintiri a wajen.

A wannan mako ne gwamnatin Najeriya ta yi kashedi ga duk masu niyyar gudana da zanga- zanga ko gangami, inda take cewa tana iya yi wa duk wani mai kunnen kashi dirar mikiya.

Gwamnatin Najeriya ta hannun ministan yada labarai Lai Mohammed da Kwamishinan ‘yan sandan Lagos, duk sun yi gargadi domin jawo hankalin mutane su kauce wa zanga zangar ta yau, amma hakan bai samu ba, ganin yadda wasu suka fito.

Hotunan da kafofin talabijin suka nuna kai tsaye daga hanyar Unguwar Lekki na dauke da jami’an ‘yan sanda cikin damara, wadanda ke kama mutane suna jefawa a cikin motocin da aka tanada.

Bayan zanga zangar bara, Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar kasashen Turai da kungiyar kasashen Afirka da Birtaniya duk sun bukaci hukumomin Najeriya da su daina amfani da karfin da ya wuce kima kan masu zanga zanga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.