Isa ga babban shafi
Najeriya

Gwamnatin Oyo ta kafa dokar takaita zirga-zirga a yankin Shasha

Gwamnatin Oyo dake kudu maso yammacin Najeriya, ta rufe kasuwar Shasha dake karamar hukumar Akinyele a Ibadan babban birnin Jihar, sakamakon fadan kabilancin da ya barke ranar Juma'ar da ta gabata a yankin.

Yankin Shasha dake garin Ibadan da aka samu rikicin kabilanci.
Yankin Shasha dake garin Ibadan da aka samu rikicin kabilanci. Daily Trust/Jeremiah Oke
Talla

Sakataren yada labaran Gwamnatin jihar ta Oyo, Mista Taiwo Adisa, ya kuma sanar da kafa dokar hana fitar dare daga karfe 6 na yamma zuwa 7 na safe, domin tabbatar da doka da oda, a yankin na Shasha da kuma ciki da kewayen kasuwar yankin.

Bayanai daga wasu majiyoyi sun ce rikicin ya samo asali ne daga cacar bakan da ta barke tsakanin wata mata mai shagon saida kayayyaki da wani mai dakon kaya, kan sharar da ya zubda a kusa da Inda take kasuwanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.