Isa ga babban shafi
Najeriya

Ministan tsaro ya bukaci 'yan Najeriya su daina jin tsoron 'yan bindiga

Ministan tsaron Najeriya Janar Bashir Magashi ya bukaci Yan kasar da su dinga kukan kura suna afkawa Yan bindigar dake kai musu hare hare a sassan kasar.

Ministan tsaron Najeriya Bashir Salihi Magashi
Ministan tsaron Najeriya Bashir Salihi Magashi Daily Trust
Talla

Magashi wanda ya bayyana takaicin sa kan sace daliban kwalejin Kagara dake Jihar Naija yace Yan Najeriya na da alhakin tabbatar da tsaron kan su da yankunan su, yayin da yake bayyana Yan bindigar a matsayin matsorata.

Tsohon hafsan sojin yace ba wai hakkin sojoji bane kawai na samar da tsaro, domin kowanne dan kasa na da rawar da zai taka wajen kare lafiyar kan sa da sauran jama’a.

Janar Magashi yace bai dace mu zama matsorata ba, domin wani lokaci wadannan Yan bindiga naas zuwa da harsasan da suka wuce guda 3 kuma da zaran sun harba su sai jama’a su ruga da gudu.

Ministan yace bai dace mu zama matsorata ba, wajen tserewa da zaran an an razana mu, saboda haka ya dace mu tsaya mu fuskance su, domin idan sun san zamu kare kan mu, zasu gudu.

Janar Magashi wanda yayi watsi da bukatar wasu na ganin an baiwa kowanne dan kasa izinin mallakar bindiga, yace ko a kasashen da suka cigaba ba, ana cigaba ad tafka mahawara kan bada izinin mallakar bindigar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.