Isa ga babban shafi
Najeriya-Tattalin Arziki

Najeriya ta gayyaci kwararru don farfado da Ajaokuta

Gwamnatin Najeriya ta bayyana shirin dauko kwararru daga kasashen waje don gudanar da binciken kwakwaf kan Kamfanin sarrafa Karafa na Ajaokuta, na biliyoyin Naira.

Kamfanin sarrafa karafa ta Najeriya na Ajaokuta
Kamfanin sarrafa karafa ta Najeriya na Ajaokuta Daily Trust
Talla

Rahotanni sun tabbatar da cewa tun a bara ya kamata ace kwararrun su iso Najeriya, to amma aka samu tsaiko saboda dakatar da tafiye-tafiye da annobar korona ta janyo.

To sai dai Jami’ai a kakakin ma’aikatar ma’adanai da bunkasa karafa ta Najeriya Ayodeji Adeyemi, ya shaida wa manema labarai cewa, yanzu haka ana ci gaba da wannan yunkuri na shigo da bakin zuwa kasar don gudanar da aikin binciken a cibiyar dake jihar Kogi.

Tun a watan Oktoban shekarar 2019 a Sochi na kasar Rasha, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya sanya hannu kan yarjejeniyar da Shugaban Rasha, Vladimir Putin, don sake farfado da Kamfanin sarrafa Karafan na Ajaokuta.

Ana saran kamfanin ya samar da guraban aikin yi har dubu 40, lokacin ya fara aiki gadan-gadan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.