Isa ga babban shafi
Najeriya-Tsaro

Makomar tsaro a tarayyar Najeriya

Kare rayuka da dukiyar jama’a na daga cikin manyan ayyukan da suka rataya akan gwamnatocin duniya, abinda ya sa wasu kasashe kan kaddamar da yaki domin kare lafiyar rayukan jama`arsu duk lokacin da suka fuskanci wani kalubale.

Mutane a titin birnin Lagos a Najeriya. Lagos na daya daga cikin biranen da ake samun masu bahaya a fili
Mutane a titin birnin Lagos a Najeriya. Lagos na daya daga cikin biranen da ake samun masu bahaya a fili Reuters / Akintunde Akinleye
Talla

A kasa kamar Najeriya, harkar tsaro ta rataya ne akan gwamnatin tarayya wadda ke da iko da sojoji da 'yan sanda da 'yan sandan farin kaya da jami’an tsaron Civil Defence da makamantan su.

Wannan ya sa a koda yaushe Gwamnonin Jihohi kan yi korafi cewar basu da ikon baiwa wadannan jami’an tsaro umurni, duk da yake sune ke iko da yankunan jihohinsu, abinda ya sa wasu daga cikinsu ke bukatar sake fasalin tsaron kasar domin basu damar kirkiro rundunar 'yan sanda ta kansu, kuma sannu a hankali, ganin yadda matsalar tsaro ke cigaba da ta’azzara a kasar, wadannan gwamnoni na samun goyan bayan jama’a.

Wani jami'in dan sanda a birnin Legas dake tarayyar Najeriya.
Wani jami'in dan sanda a birnin Legas dake tarayyar Najeriya. AP - Sunday Alamba

Yanzu haka Najeriya ta shiga wani irin yanayin da bata taba gani ba, sakamakon tabarbarewar harkokin tsaron, musamman a yankin arewacin kasar, wanda mayakan Boko Haram da 'yan bindiga barayin shanu da masu garkuwa da mutane suka hana jama’a zaman lafiya.

Yadda matsalar tsaro ke kamari a arewacin Najeriya

Rahotanni sun nuna cewar wadannan mutane dake dauke da makamai na zamani, wadanda ake cewa wani lokaci ma sun zarce na jami’an tsaron hukuma, sun yi nasarar tada garuruwa da dama ko kuma karbe iko da su a yankin arewa maso gabas da kuma arewa maso yamma.

Wani bincike da Jaridar Daily Trust ta gudanar kwanakin baya, ya bayyana yadda wadannan 'yan bindiga suka tashi garuruwa da dama a Jihar Kaduna wadanda yanzu haka suka zama kufai, wato babu kowa a cikin su, abinda ya tilastawa mazauna wadannan garuruwa komawa birane domin tsira da rayukan su.

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El Rufa'i.
Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El Rufa'i. © Twitter@GovKaduna

Ko a makon nan, rahotan da gwamnatin Jihar Kaduna ta bayar na shekarar da ta gabata, yace mutane 937 aka kashe, adadin da ya zarce wadanda Boko Haram ta kashe baki daya a bara.

Hare haren wadannan 'yan bindiga, musamman a Jihohin Kaduna da Katsina da Zamfara da Sokoto da Neja da Nasarawa da kuma Benue sun yi sanadiyar rasa daruruwan jama’a da kuma jikkata wasu da dama, yayin da daga bisani kuma batun garkuwa da mutane domin karbar diyya, abinda a shekarun baya ake danganta shi da wani yanki na Najeriya, ke neman zama ruwan dare.

Makarantar sakandaren garin Kankara dake jihar Katsina a arewacin Najeriya, inda 'yan bindiga suka sace dalibai fiye da 300, kafin daga bisani su sako su bayan kwanaki 6.
Makarantar sakandaren garin Kankara dake jihar Katsina a arewacin Najeriya, inda 'yan bindiga suka sace dalibai fiye da 300, kafin daga bisani su sako su bayan kwanaki 6. AP - Abdullatif Yusuf

A watannin da suka gabata, 'yan bindigar dake tallata kawunan su ta faifan bidiyo dauke da muggan makamai, sun kai hare hare da dama kann makarantun gwamnati a Jihohin Katsina da Zamfara da Kaduna da kuma Neja, inda suka kwashi dalibai da dama har saida aka tattauna da su kafin su sako su.

Wata mata dake jiran sake ganin danta dake cikin daliban makarantar sakandaren Kankara da 'yan bindiga suka sace.
Wata mata dake jiran sake ganin danta dake cikin daliban makarantar sakandaren Kankara da 'yan bindiga suka sace. AP - Sunday Alamba

Duk da yake babu tabbacin ko an biya kudi ko ba’a biya ba kafin kubutar da wadannan dalibai, ganin yadda wannan matsalar ke cigaba da karuwa ya sa jama’a suka fara nuna yatsa ga gwamnati da jami’an ta, inda suke zargin su da gazawa wajen sauke daya daga cikin nauyin dake kan su na kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Yayin da ake wannan sai ga bayani daga babban Jami’in gwamnatin Najeriya kuma mai baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara kan harkokin tsaro, Janar Babagana Manguno ya fito fili yana cewar shugaban kasar ya bada makudan kudade a sayo makamai amma sun yi batan dabo, saboda babu wanda ya san inda suka shiga.

Mai ba da shawara kan harkokin tsaro Babagana Monguno tare da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a fadar gwamnati da ke birnin Abuja.
Mai ba da shawara kan harkokin tsaro Babagana Monguno tare da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a fadar gwamnati da ke birnin Abuja. © Twitter@NGRPresident / Presidency Nigeria

Wannan labari mai tada hankali na zuwa ne a daidai lokacin da akasarin Yan Najeriya suka fara dawowa daga rakiyar gwamnati da jami’anta cewar za su iya kare rayukansu, ganin yadda Yan bindiga ke cin karensu babu babbaka musamman a yankin arewacin kasar.

Yau ta kai ga iyaye na fargabar tura ‘yayansu makarantu, manoma na tsoron zuwa gonakinsu, yan kasuwa na tsoron tafiye tafiye, ma’aikata na tsoron zuwa garuruwan su hutun karshen mako, yan kasuwa na fargabar tafiya kasuwannin kauyuka domin cin kasuwa, yayin da ake bin mutane har gidajen su ana kashe su da sace matansu da yaransu domin karbar diyya.

Wani magidanci Aliyu Ladan Jangebe cikin jimami kasancewar 'ya'yansa na daga cikin daliban makarantar 'yammata ta Jangebe sama da 300 da 'yan bindiga suka sace amma suka sako su bayan 'yan kwanaki.
Wani magidanci Aliyu Ladan Jangebe cikin jimami kasancewar 'ya'yansa na daga cikin daliban makarantar 'yammata ta Jangebe sama da 300 da 'yan bindiga suka sace amma suka sako su bayan 'yan kwanaki. AP - Ibrahim Mansur

An kuma samu wasu 'yan bindigar dake sanya haraji ga mazauna wasu garuruwa domin biyan kudi kafin su je su noma gonakinsu ko kuma girbe abinda suka shuka.

Wasu masana na danganta wannan matsala da karancin jami’an tsaron da Najeriya ke da shi da rashin isassun kayan aiki na zamani da kuma karuwar matsalolin tsaron da ake da su, amma kuma wasu na cewar wannan ba abin dubawa bane, ganin yadda ake da miliyoyin matasan dake bukatar daukarsu aikin tsaron kasa amma gwamnati ta kasa basu damar shiga aikin.

Yau ta kai ga har wasu 'yan Najeriya, cikin su harda 'yan siyasa da masu Sarautar Gargajiya na cewa ya dace Najeriya ta dauko sojin haya wajen tinkarar wadannan matsaloli.

Jami'an tsaron Najeriiya a harabar makarantar sakandaren Jangebe dake jihar Zamfara.
Jami'an tsaron Najeriiya a harabar makarantar sakandaren Jangebe dake jihar Zamfara. AP - Ibrahim Mansur

Wannan ba karamar yankar kauna bace ga jami’an tsaron kasar da suka taka gagarumar rawar wajen shawo kan matsalolin tsaro daban daban a ciki da wajen Najeriya, har ta kaiga sun samu lambar girmar da ake alfahari da su.

Abin tambaya anan shi ne, su wanene suke yiwa Najeriya zagon kasa wajen ganin sun lalata kasar, musamman yankin arewacin ta da aka sani da zaman lafiya, wanda a yau mutane ko gonakinsu basa iya zuwa, yayin da ake bin su cikin gidajen su ana afka musu da kuma hana ‘yayansu karatu?

Daya daga cikin dakunan daukar karatu dake makarantar sakandaren garin Jangebe dake jihar Zamfara a tarayyar Najeriya.
Daya daga cikin dakunan daukar karatu dake makarantar sakandaren garin Jangebe dake jihar Zamfara a tarayyar Najeriya. AP - Sunday Alamba

A hirarsa da Radio France Internationale, Janar Idris Bello Dambazau mai ritaya, ya bukaci gudanar da bincike domin gano wadanda suka karkata akalar makudan kudaden da aka ware domin sayan makamai domin zama darasi ga wasu masu tunanin aikata irin wannan laifi.

Tabbas, gazawa ce babba, ga hukumomin da suka kasa samarwa jama’ar su tsaro, ta yadda za su samu natsuwa a gidajensu da wuraren ayyukansu, kuma hakki na hannun shugabanni a matakai daban daban na duba wannan matsala da idon basira da zummar samo mafita cikin gaggawa, ganin yadda aka dauki dogon lokaci ana cin tuwon yau da miyar jiya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.