Isa ga babban shafi

Hare haren Boko haram ya raba mutane sama da miliyan biyu da muhallin su

A Arewa Maso gabashin Najeriya inda aka kwashe shekaru 10 ana fama da hare haren mayakan boko Haram wanda ya raba mutane sama da miliyan biyu da muhallin su, ya kuma haifar da lalacewar kayan more rayuwa da wahalar samun kula da lafiya ga mutanen da suka tsere daga gidajen su, har yanzu tsuguni bata kare ba.

Wasu daga cikin 'Yan gudun hijira a jihar Borno
Wasu daga cikin 'Yan gudun hijira a jihar Borno www.kassfm.co.ke
Talla

Kungiyoyin jinkan da suka damu da halin da mutanen yankin ke ciki sun yi kokarin janyo hankali kan tabarbarewar al’amura ganin yadda annobar korona ta dauke hankalin Duniya.

Masu aikin jinkai sun bayyana bakin cikin su kan koma bayan da ake samu na kudaden agaji daga masu taimakawa domin kula da mazauna yankin arewa maso gabashin Najeriya, ganin yadda matsalar tsaron yankin ya kwashe sama da shekaru 10 ana fama da shi.

Yanzu haka a yankin mutanen da aka raba da muhallin su na kokarin sake gina rayuwar su, kuma wadannan mutane na cigab ada fama da matsalar tsaro.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.