Isa ga babban shafi
Katsina-Gobara

Gobara ta lakume miliyoyin Naira a kasuwar Katsina

Wata gobara ta lakume tarin dukiyoyi tare da haddasa asarar miliyoyin Naira a babban kasuwar Katsina da ke Najeriya.

Yadda gobara ta lakume dukiya a Katsina
Yadda gobara ta lakume dukiya a Katsina © Tanko
Talla

Rahotanni sun ce,  gobarar ta tashi ne a sanyin safiyar yau da misalin karfe 8 da rabi,  inda ‘yan kasuwa suka yi ta rige-rigen kwashe kayayyakinsu.

Jami’an kashe gobara na ci gaba da aikin dakile ibtila'in, yayin da hotunan da aka wallafa a shafukan sada zumunta suka nuna yadda bakin hayaki ke turnuke sararin samaniya.

RFI Hausa ta tuntuni Malam Aliyu, daya daga cikin masu shaguna a kasuwar, kuma ya shaida mana cewa, wutar ta yadu a sassa daban daban na kasuwar.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren bayanin Malam Aliyu wanda ya ce, babu abin da ya tsira da shi daga wannan ibtila’in gobara.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.