Miliyoyin yaran Najeriya ba sa samun ruwa mai kyau a kullum
Yayin da ake bikin ranar ruwa ta duniya, Hukumar UNICEF ta ce kusan kashi daya bisa 3 na yaran Najeriya wato miliyan 26 da rabi ba sa iya samun tsaftacacen ruwan da suke bukata kowacce rana.
Wallafawa ranar:
Jami’in hukumar a Najeriya Peter Hawkins ya ce wannan ba wai wata sabuwar matsala ba ce domin kuwa ta dade tana addabar al'umma.
Hawkins ya ce, a inda ake fama da karancin ruwa sakamakon kafewar rijiyoyi, yara ne suka fi jin radadin matsalar ganin yadda suke wahala wajen neman ruwan, abin da ke hana su tafiya makaranta.
Dangane da yanayin samar da ruwan sha a bainar jama'a a Najeriya, Abubakar Isa Dandago ya tattauna da Daraktan Hukumar Samar da Ruwan Sha a Jihar Kano Yunusa Muhammad Inuwa.
Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakkiyar hirarsu
Yadda hukumomi ke samar da ruwan sha a Najeriya
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu