Isa ga babban shafi
Najeriya-Rigakafi-Coronavirus

'Yan Najeriya fiye da 370,000 sun karbi kashin farko na rikakafin COVID-19

Gwamnatin Najeriya ta ce 'yan kasar sama da dubu 370 ne suka karbi zagaye na farko na allurar rigakafin cutar korona da aka kaddamar. 

Allurar rigakafin AstraZeneca
Allurar rigakafin AstraZeneca REUTERS - DADO RUVIC
Talla

Hukumar kula da lafiya a matakin farko ta ce daga cikin allurai dubu 400 da kasar ta karba a matsayin kashi na farko, an yi wa mutane dubu 374,385 allurar.

Sanarwar hukumar ta ce  kowacce jiha ta karbi maganin daga cikin jihohi 36 da ake da su tare da birnin Abuja amma ban da jihar Kogi wadda bata da inda zata aje maganin saboda lalata asibitin lokacin zanga zangar matasa ta adawa da cin zarafin 'yan Sanda.

Alkaluman hukumar sun ce Jihar Lagos ta yi wa mutane kusan dubu 92 allurar, abinda ya sanya ta a matsayin ta farko, sai Jihar Ogun mai mutane dubu 36,953, sai Bauchi mai mutane dubu 31,321 sannan Kaduna mai mutane dubu 29,426.

Hukumar ta bayyana jihohin Kebbi da Taraba da Abia a matsayin wadanda ba su yi wa mutane allurar sosai ba.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.