Isa ga babban shafi
Najeriya-Tattalin arziki

Tattalin arzikin Najeriya da rauni duk da murmurewa daga masassara - Tinubu

Jagoran jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya ce duk da ficewar kasar daga masassarar tattalin arziki har yanzu tattalin arzikin Najeriya na da rauni ganin yadda ake ci gaba da samun karuwar marasa ayyukan yi. 

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da tsohon gwamnan jihar Lagos Bola Ahmad Tinubu bayan kammala wani taro kan jam'iyyar APC a fadar shugaban ta Villa da ke Abuja babban birnin kasar.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da tsohon gwamnan jihar Lagos Bola Ahmad Tinubu bayan kammala wani taro kan jam'iyyar APC a fadar shugaban ta Villa da ke Abuja babban birnin kasar. NAN
Talla

Tinubu ya ce har yanzu akwai gagarumin aiki a gaban hukumomin Najeriya wajen samar wa matasa ayyukan yi da bunkasa kayan more rayuwa da bangaren masana’antu da kuma tabbatar da habakar noma da kiwo.

Yayin da ya ke gabatar da kasida wajen taron tunawa da Sardauna Ahmadu Bello a Kaduna, Jagoran APC ya ce har yanzu akwai gagarumin aiki a gaban shugabannin kasar wajen ganin an rage yadda ake kashe kudade ta hanyar tafiyar da gwamnati da kuma gina matasa.

Tsohon Gwamnan na Lagos ya ce rashin aikin yi ya yi yawa a Najeriya duk da kokarin da gwamnatin kasar ke yi, sakamakon annobar korona, wadda ta haifar da matsala a tattalin arzikin duniya baki daya.

Jagoran ya yaba wa shugaban kasa Muhammadu Buhari kan yadda yake tafiyar da tattalin arzikin Najeriya wanda ya taimaka wajen rage radadin tsadar rayuwa, amma ya ce ko da ya ke kasar ta fice daga masassarar tattalin arziki, har yanzu tattalin arzikin Najeriya bai gama murmurewa ba, yayin da ake fama da matsalar zaman kashe wando.

Tinubu ya ce babu yadda Najeriya za ta shawo kan matsalar aikata laifuffuka ba tare da samar wa matasa ayyukan yi ba.

Tsohon Gwamnan ya ce yayin da Jihohi da Kananan hukumomi ke kokarin karkata kasafin kudin su daidai da kudaden shigar da suke samu, ya dace gwamnatin tarayya ta mayar da hankali wajen samar da ayyukan yi ga matasan da ke arewaci da kudancin kasar domin kawo karshen tashe tashen hankulan da ake samu.

Tinubu ya ce kullum biranen Najeriya cika suke da mutane, amma kuma babu ayyukan da jama’a za suyi.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.