Isa ga babban shafi
Najeriya-Pulato

Rundunar 'Yan Sandan Plateau ta tsare DPO saboda kashe Fulani makiyaya

Rahotanni daga Najeriya sun ce yanzu haka rundunar Yan Sandan kasar reshen Jihar Plateau ta kama wani DPO da jami’an sa dake aiki a karamar hukumar Bassa saboda tuhumar da ake musu na harbe wasu Fulani makiyaya guda biyu.

Fulani Makiyaya na fuskantar babban kalubale a Najeriya, musamman bayan tsanantar hare-haren 'yan bindiga da kuma ayyukan garkuwa da Mutane.
Fulani Makiyaya na fuskantar babban kalubale a Najeriya, musamman bayan tsanantar hare-haren 'yan bindiga da kuma ayyukan garkuwa da Mutane. AFP
Talla

Wannan ya sa kungiyar matasan Fulani mai fafutukar wanzar da zaman lafiya ‘Jonde Jam‘ a Nijeriya ta fara tayar da jijiyoyin wuya da nuna bacin rai akan abun da shuagaban kungiyar ta kasa baki daya Alhaji Saidu Maikano, yace suna nuna kukansu ne sakamakon yadda wannan DPO yan sanda yayi gaban kan sa wajen kashe wadannan makiyaya bayan sun dawo daga kiwo.

Alhaji Sidu Maikano shugaban kungiyar Fulanin ya nuna matukar bacin ran yan kungiyar akan wannan kisan gilla da DPO ya yiwa yaran, dangane da haka yayi kira ga Siueto Janar na yan sandan Najeriya domin ya hukunta DPO a karkashin doka ta kasa kuma ya biya diya ga iyayen yaran makiyaya.

Mukadashin kwamishinan yan sandan jihar Plateau DCP Tafida Aliyu, ya shaida mana cewar a tun da farko shi DPO ya gabatar da wani rahoton cewar sunyi a rangama da yan fashi da makamai ne abinda yayi sanadiyar kashe mutane biyu daga cikin su, amma daga baya an gano ba gaskiya ya fada ba, abinda ya sa kwamishian yan sanda ya bukaci a yi bincike kuma aka gano cewar shine ya bindige yaran makiyaya,n don haka an cafke shi an tsare shi kuma ana cigaba da masa akai.

Yanzu haka dai jama’a musamman ‘yan uwan wadannan makiya sun zuba ido suga yadda hukuma zata bi musu kadin wannan kisa da kuma hukunta wannan baturen ‘yan sanda da ake zargi da aikata wannan aika aika.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.