Isa ga babban shafi
Najeriya-Biafra

Mayakan IPOB sun sake kai farmaki ofishin 'yansanda a jihar Imo

A Najeriya wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘ya’yan kungiyar IPOP ne da ke fafutukar kafa kasar Biafra sun sake kai farmaki kan Ofishin ‘yansanda da ke jihar Imo a kudancin kasar kwana guda bayan balle gidan yarin jihar.

Tutar kungiyar IPOB mai fafutukar kafa kasar Biafra daga Najeriya.
Tutar kungiyar IPOB mai fafutukar kafa kasar Biafra daga Najeriya. STEFAN HEUNIS / AFP
Talla

Kakakin rundunar ‘yansandan jihar Orlando Ikeokwu da ke tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labaran Faransa, ya ce ‘yan bindigar sun kone Ofishin ‘yansanda na garin Ehime Mbano yau Laraba.

Jami’in bai bayyana ko akwai wadanda suka jikkata a farmakin na IPOB ba sai dai ya ce an kone motocin ofishin 3 kumus.

Farmakin kan Ofishin ‘yansanda shi ne irinsa na biyu cikin kasa da kwanaki 3 da ‘yan bindigar na kungiyar IPOB ke kaiwa ciki har da wanda suka kai kan shalkwatar rundunar da ke Owerri, baya ga kaddamar da hari kan gidan yari tare da kubutar da masu laifi fiye da dubu 1 da 800.

Tuni dai Rundunar ‘yansandan Najeriyar ta sha alwashin bin sahun ‘yan bindigar tare da kakkabe barazanarsu a yankin, bayan umarnin kame mayakan daga Babban sufeton ‘yansanda.

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo da ke ziyarar a jihar don ganewa idonsa abin da ya faru ya ja hankali kan muhimmancin zaman lafiya yayinda ya nesanta ayyukan kungiyar da manufofin al’ummar jihar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.