Isa ga babban shafi
Najeriya - Amurka

Amurka ta bukaci 'yan kasarta da su kaucewa zuwa Najeriya

Gwamnatin Amurka ta gargadi jama’ar kasar da su kaucewa tafiya Najeriya saboda laifuffukan da suka shafi ayyukan ta’addanci da tashe tashen hankula da garkuwa da mutane da kuma fashin teku.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da takwaransa na Amurka Joe Biden yayin wata ziyara da Buhari ya kai Amurka lokacin shugaba Barack Obama
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da takwaransa na Amurka Joe Biden yayin wata ziyara da Buhari ya kai Amurka lokacin shugaba Barack Obama © Presidency of Nigeria
Talla

Wata sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta wallafa a shafin ta ya bayyana cewar Jihohin Borno da Yobe da arewacin Adamawa na fama da ayyukan ta’addanci da kuma garkuwa da mutane, yayin da matsalar garkuwa da mutane kuma tayi kamari a Jihohin Bauchi da Gombe da Kaduna da Kano da Katsina da kuma Zamfara.

Sanarwar tace Jihohin dake gabar ruwa irin su Akwa Ibom da Bayelsa da Cross River da Delta da kuma Rivers na fama da matsalar manyan laifuffuka da garkuwa da mutane da kuma fashin teku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.