Isa ga babban shafi
Najeriya

Daliban jami'ar Benue sun kubuta daga hannun 'yan bindiga

Hukumomin Jami’ar Horas da Ayyukan Noma ta jihar Benue da ke Najeriya sun ce,  daliban da 'yan bindiga suka sace a makarantar sun yi nasarar kubuta.

Hoton domin misali kan 'yan bindiga.
Hoton domin misali kan 'yan bindiga. © Depositphotos
Talla

Daraktar Yada Labaran Jami’ar Rosemary Waku ta ce, biyu daga cikin daliban an sake su ne yayin da sauran kuma suka tsere daga hannun wadanda suka sace su.

Jami’ar ta gabatar da sunayen wadanda aka sake a matsayin Israel Farren Kwaghee da Solomon Salihu wadanda tuni suka koma makarantar kuma ana duba lafiyarsu, yayin da sauran da ba ta bada adadinsu ba, su ma suka kubuta.

Kakakin 'yan sandan jihar Benue Catherine Anene ta tabbatar da kubutar daliban, yayin da ta ce suna ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

Ya zuwa yanzu Jami’ar ba ta yi karin haske ko an bai wa 'yan bindigar kudi ba kafin sakin daliban lura da cewar, sun bukaci Naira miliyan 21 a matsayin diyya kafin su sake su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.