Isa ga babban shafi
Najeriya

An gano manyan mutanen dake daukar nauyin ta’addanci a Najeriya - Malami

Ministan shari’ar Najeriya Abubakar Malami ya ce binciken da suka gudanar ya nuna musu wasu fitattun 'yan Najeriya da kuma 'yan kasuwar da ke daukar nauyin ayyukan ta’addanci a cikin kasar.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da Ministan shari'ar kasar Abubakar Malami.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da Ministan shari'ar kasar Abubakar Malami. The Whistler NG
Talla

Ministan ya ce tuni aka fara shirin gurfanar da wadannan mutane a gaban kotu domin fuskantar shari’a akan rawar da su ke takawa wajen haifar da tashin hankali sakamakon binciken da gwamnati ta gudanar a Daular Larabawa dangane da masu daukar nauyin bai wa boko haram kudade.

Wannan matsayi na gwamnati na zuwa ne a dai dai lokacin da kasar ke fuskantar karuwar hare haren ayyukan ta’addanci na boko haram a yankin arewa maso gabas da kuma wasu hare haren na daban a wasu yankuna.

Malami ya ce gwamnati ta dauki dogon lokaci ta na gudanar da bincike akan wannan lamarin da ya shafi ayyukan ta’addanci bayan da kotu a Daular Larabawa ta daure wasu 'yan Najeriyar guda 6.

Ministan ya ce binciken da suka dauki dogon lokaci su na yi ya nuna musu wasu mutane da hukumomi da ke da hannu wajen jefa kasar cikin tashin hankali.

Malami ya ce suna da kwararan shaidun da ke nuna musu irin wadannan mutanen da ke daukar nauyin baiwa 'yan ta’adda kudade kuma yanzu kotu ce za ta tabbatar da wannan zargi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.