Isa ga babban shafi
Najeriya-'Yan Sanda

'Yan bindiga sun kashe 'yan sanda 13 a Akwa Ibom

Wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton ’yayan haramcaciyar kungiyar da ke fafutukar kafa kasar Biafra ta  IPOB ne sun kashe 'yan Sanda guda 7 a hare haren da suka kai yammacin juma’a a Jihar Rivers.

Wani jami'in dan sanda a birnin Legas dake tarayyar Najeriya.
Wani jami'in dan sanda a birnin Legas dake tarayyar Najeriya. AP - Sunday Alamba
Talla

Wannan ya biyo harin da ‘yayan kungiyar suka kai tashar 'yan Sandar dake Elimgbu ne,  wanda ya yi sanadiyar kashe 3 daga cikin jami’an da ke aiki, yayin da aka kashe wasu guda 2 a Cibiyar 'yan Sandan da ke Rumuji.

Rahotanni sun ce wasu Karin 'yan sandan guda biyu kuma sun mutu sakamakon harin da aka kai musu a wurin binciken ababen hawa da ke kan hanyar East-West road.

Wadannan kashe kashe na faruwa ne duk da dokar hana fitar dare da gwamnatin Jihar Rivers ta saka domin dakile hare haren da ake samu a Jihar.

A jihar Akwa Ibom ma haka abin yake, inda 'yan bindigar suka kai hari kan tashar 'yan Sandan da ke karamar hukumar Ini, inda suka bude wuta kan jami’an tsaron, suka kuma kashe da dama daga cikin su.

Rahotanni sun ce bayan harin tashar 'yan sandan, 'yan bindigar sun kuma kai hari Barikin 'yan Sandan, inda suka kashe wasu daga cikin su.

Kakakin 'yan Sandan Jihar Odiko MacDon ya tabbatar da aukuwar lamarin amma kuma yaki bada adadin jami’an da suka mutu da wadanda suka jikkata.

A makwannin da suka gabata an samu karuwar hare hare kan jami’an yan sanda a jihohin da ke Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudancin Najeriya, ciki har da wanda aka kai Babbar Cibiyar 'yan sandan Jihar Imo da kuma sakin firsinoni kusan 2,000 a Jihar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.