Isa ga babban shafi
Najeriya-Sallah

Sai a ranar Laraba watan Shawwal zai kama a Najeriya- NASRDA

Hukumar kula da sararin samaniyar Najeriya ta NASRDA ta sanar da cewar watan Ramadan zai kare ne ranar laraba mai zuwa, saboda haka ranar alhamis za ta zama ranar 1 ga watan Shawwal.

Hukumar ta ce zai yi wuya watan na Shawwal ya tsaya a sararin samaniya ranar Talata.
Hukumar ta ce zai yi wuya watan na Shawwal ya tsaya a sararin samaniya ranar Talata. Sajjad HUSSAIN AFP
Talla

Daraktan hukumar Dr Felix Ale ya ce binciken da suka gudanar ya nuna musu cewar a daren laraba 12 ga watan Mayu da misalign karfe 8.30 na dare za a ga jinjirin watan Shawwal, wanda ke nuna cewar ranar alhamis ce zata zama ranar 1 ga wata.

Idan binciken masanan wannan hukuma ya tababta, zai zama cewar za a gudanar da bikin ranar sallar Eid el Fitr ne ranar alhamis, sabanin laraba da ake ta hasashe.

Sai dai bisa ka’ida hukumar kula da harkokin shari’ar musulunci da ke Najeriya ita ke da alhakin sanar da ganin watan Ramadana da kuma kawo karshen sa domin gudanar da bikin sallar idi kamar yadda Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar ya saba gabatarwa.

Tuni wannan matsayi ya haifar da mahawara tsakanin al’ummar Musulmin Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.