Isa ga babban shafi
Najeriya - Tattalin Arziki

Dala miliyan 153 EFCC ta kwato daga tsohuwar ministar man Najeriya - Bawa

Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC, AbduRashid Bawa, ya ce kawo yanzu hukumar tayi nasarar kwato dala miliyan 153 daga hannun tsohuwar ministar kula da albarkatun man fetur ta kasar Diezani Alison Madueke.

Tsohuwar Ministar kula da albarkatun man Najeriya, Diezani Alison Madueke.
Tsohuwar Ministar kula da albarkatun man Najeriya, Diezani Alison Madueke. AP - Ronald Zak
Talla

Shugaban na EFCC da yayi karin bayanin cikin mujallar da hukumar ta wallafa a watan Afrilu, ya kara da cewar sun kuma kwace wasu gidajen daga hannun tsohuwar Ministar Kudin da darajar su ta kai dala miliyan 80.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da shugaban hukumar yaki da cin hanci da rasahawa ta EFCC AbduRashid Bawa
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da shugaban hukumar yaki da cin hanci da rasahawa ta EFCC AbduRashid Bawa © The Guardian Nigeria

Bawa ya kuma ce akwai wasu shari’o’in dake gudana yanzu haka kan laifukan almundahanar makudan kudade a Najeriya, ciki har da batun cin han ci da rashawar kimanin dala miliyan 115 kan sha’anin zabe.

Tun cikin watan Fabarairun da ya gabata hukumar EFCC a karkashin tsohon shugabanta Ibrahim Magu, ke neman hukumomin Birtaniya, inda a can ma take fuskantar shari’a, da su miko mata Mis Diezani domin ta fuskanci shari’a akan tuhumar wawashe akalla dala biliyan 2 da rabi daga baitulmalin gwamnati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.