Ganduje ya yi wa fursunoni sama da 100 afuwa saboda bikin sallah Ƙarama
Gwamna jihar Kano a Najeriya Abdullahi Umar Ganduje ya yi wa fursunoni 123 afuwa albarkacin bukukuwar Karamar Sallah, bayan kammala azumin watan ramadana.
Wallafawa ranar:
Gwamnan wanda ya kai ziyara gidan yarin da ke Goron Dutse a ranar Alhamis, ya ce wadanda aka yi wa afuwar an zabe su ne bisa irin girman laifinsu da kuma alamun halayya ta gari da suka nuna.
A cewarsa, wannan ziyara wata manuniya ce ga daurarru dake tsare domin su san cewa gwamnatin Jihar bata manta da su kuma tana ci gaba da daukarsu a matsayin al’ummar jihar.
Ganduje ya ce, wannan wani yunkuri tabbatar da shirin Gwamnatin Tarayya na kokarin ganin an rage cunkoso a gidajen yarin kasar.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya Ambato Gwamnan yana shawartar fursunonin da aka yi wa afuwa da su dabi’antu da hallaya ta mutanen kirki sannan su yi wa Najeriya addu’ar samun zaman lafiya mai dorewa.
Kazalika, Ganduje ya bayar da Naira dubu biyar ga kowane daya daga cikin fursunonin da ya yi wa afuwa domin su samu kudin motar koma wa gidajensu.
A nasa jawabin, Kwanturolan Gidajen Yarin Kano, Suleiman Suleiman, ya yi wa Gwamnan godiya bisa ga wannan karamci na ’yantar da dubban fursunoni tun bayan hawansa kujerar gwamnatin jihar.
Baya ga haka, Ganduje ya kai ziyara gidan ladabtar da kananan yara da kuma na marayu a jihar Kano.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu