Isa ga babban shafi
Zaben Najeriya

Matsalar tsaron Najeriya na haifar da cikas ga shirin zaben 2023 - INEC

Hukumar zaben Najeriya ta bayyana fargaba kan yadda hare-hare kan jami’anta ke haifar da cikas ga shirye-shiryenta na tukarar babban zaben kasar na 2023.

Farfesa Mahmood Yakubu, shugaban hukumar zaben Najeriya.
Farfesa Mahmood Yakubu, shugaban hukumar zaben Najeriya. AP
Talla

Tuni dai shirye-shiryen zaben ya fara kankama tsakanin Jam’iyya mai mulki ta APC a Najeriyar da kuma babbar jam’iyyar adawa ta PDP, wadanda ke kokarin lalubo wanda zai maye gurbin shugaba Muhammadu Buhari da zai karkare wa’adinsa na biyu na tsawon shekaru 8 a mulkin kasar.

Sai dai sanarwar hukumar zaben ta Najeriya INEC ta ce akwai kalubale a tattare da shirye shiryen tunkarar zaben, sakamakon tsanantar hare-hare kan jami’anta da kuma kone tarin kayayyakin aiki tare da sace wasu.

Hukumar ta ce ko cikin watan jiya sai da aka kaiwa jami’anta 4 farmaki tare da kone tarin kayayyakin aiki, ba kuma tare da sanin wadanda ke da hannu a farmakin ba, lamarin da hukumar ke bayyanawa a matsayin babbar barazana.

Cikin watan Afrilun da ya gabata, hukumar ta INEC ta sanar da cewa zaben 2023 zai gudana ranar 18 ga watan Fabarairu, yayinda ta sha alwashin kammala shirye shiryen tunkararsa kafin karshen shekarar da muke ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.