Isa ga babban shafi
Najeriya-Zabe

Najeriya: PDP ta fara fuskantar rikicin cikin gida gabanin zaben 2023

Yayin da zaben shekarar 2023 ke kara karatowa a Najeriya, Babbar Jam’iyyar adawar kasar ta PDP na cigaba da fuskantar matsalolin cikin gida inda wasu daga cikin jiga jigan ‘yayan ta ke ficewa suna komawa Jam’iyyar APC mai mulki.

Rikici ya dabaibaye babbar jam'iyyar adawar Najeriya PDP.
Rikici ya dabaibaye babbar jam'iyyar adawar Najeriya PDP. Premium Times
Talla

Wannan ya biyo bayan sauya shekara da Gwamnan Jihar Cross River Ben Ayade yayi yau daga Jam’iyyar ta PDP da ta bashi damar hawa karagar mulki zuwa Jam’iyya mai mulki ta APC.

Rahotanni sun ce Ayade ya bayyana sauya shekar ne bayan ganawar da yayi da wasu takwarorin sa a birnin Calabar da suka kunshi shugaban Gwamnonin kasar Kayode Fayemi na Jihar Ekiti da shugaban Gwamnonin Arewa Simon Lalong da Gwamnan Jihar Imo Hope Uzodinma da kuma takwaran san a Jigawa Abubakar Badaru tare da shugaban Jam’iyyar na riko Mai Mala Buni, Gwamnan Jihar Yobe.

Wannan na zuwa ne bayan sauya shekara da Gwamnan Ebonyi David Umahi yayi daga PDP zuwa APC, yayion da takwaran sa na  Edo Godwin Obaseki ya bar APC zuwa PDP lokacin da ta hana shi tsayawa takarar wa’adi na biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.