Najeriya-'Yan bindiga
Najeriya: 'Yan bindiga sun kashe direban sarkin Birnin Gwari
A Najeriya a ‘yan bindiga a jiya Asabar, sun kashe direban sarkin Birnin Gwari a jihar Kaduna a kan hanyarsa ta zuwa Birnin Gwarin, suka kuma kona motar kurmus.
Wallafawa ranar:
Talla
Rahotanni sun ce lamarin ya auku ne da misalin karfe 3 na ranar Asabar a yayin da direban yake dawowa daga Kaduna, inda ya kai gyarar motar.
Majiyoyi daga fadar sarkin sun ce direban shi kadai ne a motar a yayin harin da ya auku a yankin gandun dajin Yako, inda wasu ‘yan bindiga suka bude wa tawagar sarkin, Zubairu Jibril Mai Gwari wuta a watan Maris, amma aka yi dace baya cikin motar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu