Isa ga babban shafi
Najeriya-Boko Haram

Najeriya za ta fara shari'ar mayakan Boko Haram

Gwamnatin Najeriya ta kammala shirin fara yi wa wasu mutane 800 da ake zargin cewa Boko Haram ne shari’a da zaran ma’aikatan kotuna sun janye yajin aikinsu.

Wasu mayakan  Boko Haram
Wasu mayakan Boko Haram AFP
Talla

Wata darakta a ma’aikatar shari’ar kasar Chioma Onuegbu ta bayyana haka, inda take cewa wadannan mutane 800 na daga cikin mutane 1,000 da ake zargin suna da hannu wajen ayyukan kungiyar ta Boko Haram, kuma tuni aka kammala gudanar da bincike a kansu.

Jami’ar ta ce wadanda ake zargin na tsare a wajen tsare masu aikata laifuffuka na soji da ke birnin Maiduguri, yayin da aka kammala shirya shaidun da za a gabatar a kansu.

Daraktar ta kuma bayyana cewar Ma’aikatar Shari’ar ta bada umurnin sakin mutane 170 da ake tsare da su saboda rashin gamsassun shaidu dangane da zargin da ake musu.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da gwamnatin Najeriya ke gurfamar da mutanen da ake zargi da hannu wajen kai hare haren kungiyar Boko Haram a gaban kotu ba.

Ko a watan jiya, Ministan Yada Labaran kasar Lai Mohammed ya sanar da cewar jami’an tsaro sun yi nasarar kama mutane akalla 400 da ke da hannu wajen bai wa kungiyar kudaden gudanar da ayyukanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.