Isa ga babban shafi
Najeriya-Fasaha

Najeriya na gab da fara kera jiragen sama

Yunkurin Najeriya na shiga cikkin jerin kasashen da ke kera jiragen sama na samun ci gaba, inda a yanzu hukumomi suka fara aikin tantance sahihancin jiragen sama masu saukar ungulu da aka kera a kasar.

Samfurin Jirgin mai saukar ungulu da za a yi gwajin sa a Najeriya
Samfurin Jirgin mai saukar ungulu da za a yi gwajin sa a Najeriya © The Guardian
Talla

Jaridar Daily Trust da ake wallafawa a Najeriya ta ce yanzu haka wannan aikin ya yi nisa, domin ya kai matakin gwaji.

Mataimakin shugaban gudanarwar hukumar NASENI da ke aikin samar da jiragen,  Engr. Mohammed Sani Haruna ya ce, kofarsu a bude take domin karbar shawarwari daga ma’aikatar da ke kula da sufurin jiragen sama kan yadda za su inganta kirar tasu domin samar da jiragen kamar yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umurni.

Engr. Haruna ya ce fatarsu ita ce samar da jiragen ingantattu kirar Najeriya wanda duniya za ta amince da su domin taimaka wa tatatlin arzikin Najeriya.

Jami’in ya ce suna da kwararrun ma’aikata da ke aiki tukuru wajen ganin sun fitar da kitse a wuta domin samar da jiragen.

Mataimakin Daraktan Sashen Kere Kere na hukumar Engr. Emmanuel Ajani ya ce suna hadin kai da kamfanin hada jiragen saman Thins da ke kasar Belgium wadanda suka horar da ma’aikatansu domin samar da jiragen.

Shugaban tawagar ma’aikatan sufurin Najeriya da ya gane wa idansa wannan gagarumin aikin da NASENI ke yi, Asaniyan Taiwo ya yaba wa hukumar saboda abin da suka gani, inda ya ce aikin zai daga darajar Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.