Isa ga babban shafi
Najeriya-NNPC

NNPC ta kulla kwantiragi da kamfanonin mai 4 don bunkasa tattalin arziki

Kamfanin NNPC a Najeriya ya sanar da kulla wani kwantiragin cinikayya tsakaninsa da wasu kamfanonin mai na Duniya 4 da suka kunshi Shell da Exxon da Total da kuma Eni, yarjejeniyar da za ta kai ga zuba jarin dala biliyan 10 a kasar.

Wani sashe na kamfanin NNPC a Najeriya.
Wani sashe na kamfanin NNPC a Najeriya. AFP/Archivos
Talla

Najeriyar mai arzikin mai fetur kuma mafi fitar da shi ketare tsakanin takwarorinta kasashen Nahiyar Afrika sabuwar yarjejeniyar wadda za ta kawar da rikicin da ta fuskanta tsakaninta da kamfanonin man a baya, za ta taimaka wajen zuba jarin tsabar kudi har dala biliyan 10 baya ga kara yawan kudaden shigar da kasar ke samu ta bangaren mai da kuma samar da ayyuka.

Wasu bayanai na nuna cewa tun a talatar da ta gabata, Kamfanin man Najeriyar na NNPC da kamfanonin man 4 da suka kunshi Shell da Exxon da Total da kuma Eni sun rattaba hannu kan yarjejeniyar hakar man a Bonga, karkashin lasisin OML 118 da ya sahale bayar da hayar filayen hakar mai.

Najeriyar wadda yanzu haka tattalin arzikinta ke tangal tangal sakamakon rashin daidaituwar farashin mai a kasuwar Duniya sanadiyyar annobar covid-19 sabuwar yarjejeniyar hakar man a karkashin ruwa tsakaninta da kamfanonin 4 za ta karan kudin shigar da bangaren mai ke bai wa kasar zuwa dala biliyan 780 baya ga wasu dala biliyan 9 ta daban.

Shugaban kamfanin na NNPC a sakon da ya wallafa a Twitter bayan kulla yarjejeniyar ya ce matakin zai nunawa Duniya cewa kofa a bude ta keg a masu son zuba jari a kasar.

Yankin na Bonga wanda ya koma samar da ganga dubu 90 kowacce rana tun daga watan Fabarairu sabanin ganga dubu 225 da ya ke samarwa a baya, yarjejeniyar za ta bayar da damar ninka ayyukan da ya ke.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.