Daliban da aka sace a Kaduna sun kubuta daga hannun Yan bindiga
Rahotanni daga Najeriya sun ce daliban Jami’ar Greenfield ta Jihar Kaduna da aka sace ranar 20 ga watan Afrilu sun yi nasarar kubuta daga hannun 'Yan bindigar da suka sace su.
Wallafawa ranar:
Kakakin Jami’ar Kator Yengeh yace dalibai 14 suka kubuta daga hannun Yan bindigar yau asabar ba tare da yin Karin bayani dangane da kudin fansar da aka biya domin kubutar da suba.
Gwamnatin Jihar Kaduna dake Najeriya taki shiga tattaunawa da Yan bindigar domin kubutar da su saboda matsayin da at dauka na kin biyan kudin fansa ga Yan ta’adda.
Rahotanni sun ce yan uwa da iyayen daliban sun yi ta fadi tashi domin tattara kudaden fansar da yan bindigar suka bukata amma ya zuwa yanzu babu tabbacin abin baiwa Yan bindigar kudi ko kuma a’a.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu