Isa ga babban shafi
Najeriya - Muhalli - Kiwo

Yadda siyasa ta yiwa Fulani makiyaya illa a Najeriya

Maganar kiwo da Fulani makiyaya suka kwashe shekaru aru-aru suna gudanarwa a Najeriya yau ya zama daya daga cikin manyan batutuwan da suka raba kan jama’ar kasar saboda abinda suka kira illar dake tattare da shi.

Wasu Shanu mallakin Fulani makiyaya yayin kiwo a wani yanki dake wajen jihar Kaduna.
Wasu Shanu mallakin Fulani makiyaya yayin kiwo a wani yanki dake wajen jihar Kaduna. AFP/Getty Images - Stefan Heunis
Talla

Sakamakon aikata laifuffuka da ake zargin wasu bata-garin Fulani makiyaya na aikatawa a wasu yankunan kasar yau ta kai ga haramta kiwo baki daya a yankunan kudancin Najeriya, yayin da wasu jihohi a yankin arewa ta tsakiya ke daukar irin wannan mataki ba tare da tsara yadda za a tsugunar da Fulani makiyayan ba, domin ganin sun ci moriyar sabbin dabarun zamani na kiwon da masana harkar noma da gwamnatin tarayya suka amince da shi.

Gwamnatin Najeriya a karkashin shirin ta na samar da wuraren kiwo na zamani da ma’aikatar kula da dabbobi ta tarayya ke lura da shi ya samo hanyar da za a taimakawa Fulani makiyaya gudanar da harkokinsu ba tare da yawo ba, matakin da ake ganin zai kawo karshen rikicin da ake samu tsakaninsu da manoma akai-akai, amma wasu gwamnonin kasar sun sa kafa sun shure, inda suka ce ba zasu bada filin da ake bukata domin gudanar da harkokin kiwon ba.

Kungiyar dake sanya ido kan rikice rikice a duniya ta ‘International Crisis Group’ wadda tayi nazari kan shirin gwamnatin Najeriyar na samar da wuraren kiwon na zamani, ta yaba da matakin ganin irin tanade-tanaden da akayi a cikin sa wanda zai kwantar da hankalin manoma da makiyayan baki daya.

Sai dai kungiyar tace abin takaici, a yayin da gwamnati ta gaza wajen wayar da Fulani makiyaya da kuma manoma domin fahimtar anfanin da shirin ke da shi, 'yan siyasa na anfani da damar wajen gargadin manoma cewar za a kwace wani kaso ne na filayen noman su domin baiwa makiyayan, abinda ya sa su adawa da shirin baki daya.

Wasu Fulani makiyaya a Najeriya
Wasu Fulani makiyaya a Najeriya REUTERS/Akintunde Akinleye

Yanzu haka dai wasu jihohin arewacin Najeriya sun bayyana niyyar rungumar wannan shiri wajen samar da filayen da za a tsugunar da makiyayan da kuma samar musu abincin dabbobi da ruwan sha da kuma makarantun da suke bukata.

Daga cikin jihohin da suke sahun gaba wajen wannan aiki har da jihar Gombe, wadda ta ware wani katafaren filin da zai dauki shanu sama da miliyan 2 ta kuma fara shuka ciyawar zamani da gina rijiyoyin samar da ruwan sha ga dabbobi na zamani tare da gina hanyoyin mota da samar da jami’an kula da dabbobi da na tsaro a yankin domin tsugunar da Fulanin jihar su.

Wannan shiri na Gombe da ake gudanarwa a dajin Wawazange kamar yadda kwamishinan kula da noma da kiwo na Jihar Alh Muhammadu Magaji ya bayyana ya samu karbuwa daga makiyaya da dama wadanda suka rungumi shirin wajen tsugunar da dabbobinsu.

Ko a wannan mako sanda gwamnatin tarayya ta tura tawaga ta musamman domin zuwa ta ganewa idanun ta yadda wannan wuri ke aiki da kuma nasarar da Jihar Gombe ta samu wajen tsugunar da makiyayan.

Wani Bafulatani makiyayi yayin kiwon dabbobinsa a jihar Kaduna dake arewa maso yammacin Najeriya. 22/2/2017.
Wani Bafulatani makiyayi yayin kiwon dabbobinsa a jihar Kaduna dake arewa maso yammacin Najeriya. 22/2/2017. © AFP

Wani masanin kula da kiwon dabbobi kuma tsohon Darakta a ma’aikatar gona a Najeriya, Dakta Junaid Maina ya tabbatar da shigar siyasa da kabilanci da kuma addini wajen harkokin kiwon da Fulani makiyaya ke yi.

Dakta Maina ya ce Najeriya na da wadataccen filin da zai dauki jama’ar kasar miliyan 200 da kuma akalla shanu miliyan 20 da ake da su, ba tare da musgunawa wani bangare ba, idan aka kawar da siyasa cikin lamarin.

Shanu a filin kiwon zamani na Gongoshi dake jihar Adamawa a yankin arewa maso gabashin Najeriya. 12/4/2021. Filin kiwon na Gongoshi daya daga cikin filayen da gwamnatin tarayyar Najeriya ta ware domin aiwatar da shirinta na tsungunar da Fulani makiyaya don kawo karshen rikicin manoma da makiyaya.
Shanu a filin kiwon zamani na Gongoshi dake jihar Adamawa a yankin arewa maso gabashin Najeriya. 12/4/2021. Filin kiwon na Gongoshi daya daga cikin filayen da gwamnatin tarayyar Najeriya ta ware domin aiwatar da shirinta na tsungunar da Fulani makiyaya don kawo karshen rikicin manoma da makiyaya. © CRISISGROUP/Akinade Akintayo Jeremiah

Yanzu haka dai jihohin da suka hada da Kano, Sokoto, Katsina, Niger da Adamawa da kuma Bayelsa, sun amince da sabon shirin tsugunar da Fulani makiyayan, yayin da sauran jihohohin arewacin kasar ke jan kafa, bayan jihar Benue da tace ba ta goyan bayan shirin baki daya.

Kungiyar International Crisis Group tace muddin aka gaza shawo kan wannan matsala a cikin wannan shekara ta 2021, batun siyasa da shirin zaben shekarar 2023 zai mamaye tsarin kuma wannan gwamnati mai ci ba zata iya warware rikicin dake cigaba da haifar da tashin hankali da kuma rasa rayuka a wasu yankuna ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.