Isa ga babban shafi
Najeriya-Kwaya

NDLEA ta kwace kwaya ta Naira biliyan 90 a Najeriya

Hukumar Yaki da Sha da kuma Safarar Miyagun Kwayoyi ta NDLEA a Najeriya ta sanar da kwace kwayar da kudinta ya kai Naira biliyan 90 a cikin watanni 4 tare da kama mutane 2,175.

Wasu daga cikin ma'aikatan NDLEA a Najeriya
Wasu daga cikin ma'aikatan NDLEA a Najeriya © ©dailypost.ng
Talla

Shugaban hukumar janar Muhammadu Buba Marwa ya bayyana haka sakamakon sabbin dabarun yaki da masu hada-hada da kwayoyin da suka kaddamar wanda ya taimaka musu wajen samun nasara.

Marwa ya ce wannan nasara da suka samu a cikin watanni 4 ya kawar da duk wani shakku da jama’a ke da su kan kokarinsu na shawo kan matsalar amfani da kwayoyin a cikin kasar.

Shugaban hukumar ya jinjina wa ma’aikatansa kan jajircewarsu wajen ganin an samu nasarar da yake magana akai, wanda ya ce zai taimaka gaya wajen dakile illar da kwayoyin ke yi wa jama’a.

Janar Marwa ya ce sun gabatar da kararraki 2,100 a kotuna kuma sun samu hukunce-hukunce sama da 500 daga cikinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.